Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Lahadi 17/12/2023 – 04/06/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya aike da ta’aziyyarsa kan rasuwar sarkin Kuwait.

Hukumar NCDC mai yaki da cututtuka ta tabbatar da bullar zazzabin Dengue a jihar Sokoto.

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja da ayyana zaben mazabar Yabo/Shagari wanda bai kammala ba a jihar Sokoto.

Sarakunan Hausawa a Kudu maso Yamma sun gargadi shugabannin siyasa da kada su cinnawa Najeriya wuta saboda zaben gwamnan jihar Kano.

Al’ummar garuruwan Dantsuntsu da Nahuta a yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina sun koka kan yadda hare haren ‘yan bindiga ke hana su girbe amfanin gona.

Oba Sikiru Kayode Adetona na na Ijebuland, jihar Ogun ya naÉ—a tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai sarautar Gbobaniyi na Ijebuland.

Wani direban ‘Keke Napep’karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe ya samu kyautar dubu 100 saboda tsananin tsoron Allah da ya nuna ya maida tsintuwar naira miliyan 9 da ya yi.

‘Yan bindiga sun sace tare da kashe mutane a akan hanyar zuwa karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a daren jiya.

An sake kwantar da dan wasan firm na kudu John Okafor don sake gutsure wani sashi na kafarsa bayan yanke ta a watan da ta gabata.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga harkokin siyasa.

Chadi ta bai wa ma’aikatan diflomasiyyar Sudan wa’adin awa 72 su fita daga kasar.

Rundunar sojojin ruwan Senegal ta kama tan uku na hodar iblis.

An yi jana’izar É—an Isra’ila da sojojin Æ™asar suka kashe bisa kuskure a Gaza.

EPL: Everton ta sami nasara akan Burnley da ci 2:0 a wasan jiya.

Laliga: Barcelona da Valencia sun tashi 1:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *