EFCC ta sake bude shari’ar zargin Rabi’u Kwankwaso, Ayodele Fayose da wasu tsaffin gwamnoni 11 da ke damfarar sama da N772bn.
Alfijir labarai ta rawaito Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma mika wa wasu tsofaffin Ministoc,i kuma a halin yanzu tana binciken N81.6bn da ake zargin an wawure a ma’aikatar agaji da yaki da fatara.
A ranar Lahadin nan ne hukumar tace wasu dala biliyan 2.2 na nufin siyan makamai domin tallafawa yakin da ake yi da ‘yan ta’adda amma wadanda ake zargin sun batar da su ta hanyar karkatar da kudade tare da tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki; marigayi dan jarida, Raymond Dokpesi, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa; da tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda da dai sauransu.
Yayin da Dasuki ke tsare a hannun jami’an tsaro na farin kaya a shekarar 2015, EFCC ta kama Dokpesi, Bafarawa, Yuguda da sauransu.
An kama su ne bayan da kwamitin shugaban kasa da ya binciki sayan makamai a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tuhume su.
The Punch
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl
Hakan baikamataba