Jam’iyyar NNPP Ta Magantu Kan Maganar Dakatar Da Gwamna Abba Yusuf A Kano

FB IMG 1713292953070

Kwamitin Koli na Ƙasa, NWC, na jam’iyyar NNPP, ya musanta zargin dakatar da Gwamna Abba Yusuf na Kano daga jam’iyyar.

Alfijir Labarai ta ruwaito Shugaban jam’iyyar na riƙo na kasa, Dr Ahmed Ajuji, da yake magana a wata hira da manema labarai a jiya Alhamis a Abuja, ya ce NNPP ba ta da wani dalilin dakatar da Yusuf daga jam’iyyar.

“A iya sanina, Gwamna Yusuf cikakken dan jam’iyyarmu ne kuma cikakken jakadan NNPP, wanda shugabancinsa da nasarorin da ba a taɓa samu ba a jihar Kano abin alfahari ne a gare mu, don haka ba mu da wani dalili na dakatar da shi.

“A zahiri, NNPP ba ta dakatar da gwamnan mu ba,” in ji shi.

Ajuji ya bayyana wadanda ke ikirarin dakatar da Yusuf daga jam’iyyar NNPP saboda halartar babban taron jam’iyyar NNPP a matsayin ‘yan wasan barkwanci kuma ƴan barandan wasu masu neman suna.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *