Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe wasu coci-coci guda uku saboda suna damun jama’ar yankunansu da kara.
Alfijir Labarai ta rawaito da yake rufe cocinan a birnin Ibadan, mashawarcin gwamnan jihar kan muhalli, Farook Akintunde, ya ce an sha gargadin aike wa cocinan takardar gargadi da kuma zaman tattaunawa da cewa su daina hana jama’a sakat amma suka ki.
Akintunde ya ce an samu cocin Christ Apostolic da ke yankin Gbogunmi yana amfani da manyan sifiku a lokacin ibadar yamma da na tsakar dare, wanda karar sifikun ke hana jama’ar unguwar sukuni.
“Duk kokarinmu na ganin shugabannin cocin sun kiyaye lamarin ya ci tura, amma babu gwamnatin da za ta zura ido ana cutar da lafiyar al’ummar da take shugabanta,” in ji Akintunde.
Daga nan ya yi gargadin cewa wuraren ibada su daina damun jama’a da kara, saboda gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa wajen rufe duk wanda ya saba dokar ba.
Hakazalika ya yi kira ga masu neman hana ma’aikata zartar da aikinsu cewa su daina ko kuma su dandana kudarsu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk