Tsohuwar Jarumar Fim nan mai dogon zango wato “Labarina” Maryam Waziri wacce aka fi sani da Layla a cikin shirin ta yi hatsarin mota tare da mijinta.
Alfijir labarai ta rawaito Mijin Maryam Waziri shi ne tsohon ɗan wasan ƙwallon kafa na Super Eagles ta Najeriya, Tijjani Babangida, kuma hatsari ya rutsa tare da dan karamin dansu da kuma kanin mijin nata.
Iyalan sun yi hatsarin ne akan hanyar Kaduna zuwa Zaria kuma anan take ƙanin Tijjani wato Ibrahim Babangida ya rasu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka Maryam da mijinta da danta suna kwance asibiti suna samin kulawar likitoci.
Maryam Waziri ta taka rawa sosai a cikin shirin labarana zango na farko, kafin daga bisani ta yi aure.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl