Masarautar Gaya a Jihar Kano ta nada Alhaji Munzir Yusuf Ali a matsayin sabon Sarkin Malaman Gaya.
Alfijir labarai ta rawaito an nada shi ne biyo bayan rasuwar mahaifinsa Sheikh (Dr) Yusuf Ali, fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya watanni shida da suka gabata, wanda shi ne mai rike da sarautar kafin rasuwarsa.
Takardar nadin mai dauke da kwanan watan 8 ga Mayu, 2024 wadda Wamban Gaya, Alhaji Mansur Ibrahim Gaya ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai, na sanar da sabon Sarkin Malaman Gaya, Alhaji Munzir Yusuf Ali, ranar da za a yi taron bikin nada sarautar kamar yadda Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya ya umurta.
Sanarwar ta hakaito cewa za a yi bikin nadin ne a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024 da misalin karfe 10 na safe a Fadar Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya.
Masarautar ta kuma shawarci sabon Sarkin Malaman na Gaya da ya ci gaba da shirye-shirye don tabbatar da nasarar nadin nasa tare da yi masa addu’ar fatan alheri da nufin Allah Ya yi masa jagoranci a wannan mukami.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl