Tirka-Tirka: CBN Ya kori ma’aikata 200 da suka hada da manyan ma’aikata da daraktoci

IMG 20240525 WA0102

Daga Aminu Bala Madobi

Akalla jami’an babban bankin Najeriya CBN 200 ne aka sallama daga aiki a ranar Juma’a 24 ga watan Mayun 2024.

Alfijir Labarai ta rawaito wannan ƙari ne ga dogon jerin abubuwan da ke gudana a cikin babban bankin koli awani mataki na saisaita ayyukan cibiyar hada-hadar kudin.

Jerin sunayen ma’aikata 117 da bankin ya kora daga ranar 15 ga Maris zuwa 11 ga Afrilu, 2024, tuni suka san inda dare yayi musu.

Wani babban ma’aikaci, wanda ya nemi a sakaya sunansa a bankin, ya tabbatar da faruwar lamarin a daren Juma’a.

“Sama da ma’aikata 200 ne aka fitar da wasikun sallama daga babban bankin Najeriya ranar Juma’a.

“Duk da haka, ba a tabbatar da adadin ma’aikatan da aka kora ba”, in ji shi.

Wasikar sallamar da wakilinmu ya samu kuma ma’aikatar kula da ma’aikata ta fitar a ranar 24 ga Mayu, 2024, ta nuna cewa manufar hakan ita ce sake tsara banki don gudanar da ayyuka masu inganci.

Wasikar, mara dauke da sa hannu, ta ce, “An fidda sabon tsarin dabarun bankin. Dangane da sabon manufarmu da hangen nesa, bankin a halin yanzu yana gudanar da wani gagarumin tsari na sake fasalin bankin.

“Sakamakon wannan bita, an umurce ni da in sanar da ku cewa ba a buƙatar ayyukanku  daga ranar Juma’a, 24 ga Mayu, 2024. Za a ƙididdige haƙƙin ku na ƙarshe kuma za a biya ku nan gaba. Na gode”

A halin da ake ciki, sabon korar ta kara ga ma’aikata 117 da babban bankin ya kora daga ranar 15 ga Maris zuwa 11 ga Afrilu, 2024.

A cikin watan Fabrairu, akalla ma’aikatan babban bankin Najeriya 1,500 ne aka mayar da su daga hedikwatar da ke Abuja zuwa ofishinsa na Legas.Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *