Yadda Aka Bada Cin Hanci Na Kimanin Biliyan 700 A Nijeriya Shekarar 2023 – In Ji ICPC

IMG 20240630 WA0203

Shugaban Hukuma Mai Zaman Kan ta da ke Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka, ICPC, Musa Aliyu, ya yi nazari kan yanayin cin hanci da rashawa a kasar nan.

A cewarsa, an bada cin-hanci da rashawa har sau miliyan  87 da kuɗin ya kai Naira biliyan 700 da aka biya a shekarar 2023.

A cewar sa, yankunan karkara ne ke bada cin hanci fiye da na birane.

Shugaban hukumar ta ICPC, ya ce cin hanci da rashawa shi ne babban cikas ga ci gaban Najeriya, inda ya kara da cewa, hakan na zubar da amincewa da hukumomin gwamnati, da zagon kasa ga bin doka da oda, da kuma dakile ci gaban tattalin arziki.

Da yake jawabi a wani taron da tsangayar fannin shari’a ta Jami’ar Ahmadu Bello ta shirya, Aliyu, Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya bayyana cewa cin hanci da rashawa lamari ne na shari’a da zamantakewa da ke bukatar cikakken tsari wajen yakar sa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *