Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce za su zauna da manyan attajirai da yan kasuwa da ƴan siyasa da masu fada aji a yankin Arewa domin lalubo hanyar magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Alfijir labarai ta ruwaito Shettima ya baiyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta RFI Hausa a makon da ya gabata.
A wani faifen bidiyo na hirar da ya karaɗe shafukan sadarwa, Kashim ya ce za su tara masu ruwa da tsaki a kowanne fanni da ke yankin domin kawo gyara ga Arewa ba tare da duba da banbancin siyasa ba da addini ba.
“Za mu zauna, zamu nemi attajiran mu kamar su Alhaji Aliko Dangote da Abdussamad Bua , za mu kira Alhaji Dahiru Mangal, za mu nemi Alhaji Muhammad Indimi, za mu nemi TY Danjuma da AYM Shafa da A A Rano da Rahmaniyya da Isa Gerawa”.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kara da cewa “za mu nemi manyan ƴan siyasa da su ka hada da; Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Aliyu Wammako da irin su Aminu Waziri Tambuwal, kun ga dan PDP ne ma, to amma ba siyasa ba ne abun, don neman mafita yankin mu ne na Arewa.
“Kuma za mu yi shi da gaske, a aikace. Ba za mu zauna mu sha shayi mu tattauna mu tashi kawai ba tare da an gani a kasa ba,” in ji Shettima.
DAILY NIGERIAN HAUSA ta gano cewa yankin Arewa dai na fama da ayyukan ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, gami da tsananin talauci da yawaitar yara da ba sa zuwa makaranta
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj