Bayanan hoto,Mako uku kenan bayan ‘yan bindigar sun sace sarkin a kan hanyarsa ta komawa gida daga garin Sokoto
Rahotonnin da muka samu daga jihar Sokoto a arewacin Najeriya na cewa Ć´an bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, sun kashe shi.
A cikin wannan makon ne sarkin aka ga sarkin a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya ‘yan bindigar kuÉ—in fansar da suka buĆ™ata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.
Mako uku da suka wuce ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da sarkin a yankin Kwanar Maharba lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.
A hirarsa da BBC, Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne magajin garin na Gobir kuma É—aya daga cikin masu naÉ—in sarki, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.
“Labarin da na samu shi ne ‘yan bindigar sun harbe shi ne tun a jiya [Talata] bayan la’asar, kuma waÉ—anda suka je tattauna biyan kuÉ—in fansa ne suka ga gawar sarkin a kwance,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da aka yi magana da shi ba su karɓi gawar mai martaban ba tukunna.
Kazalika, ya ce akwai É—an sarkin mai suna Kabiru da aka yi garkuwa da su tare, kuma abin da suka saka a gaba kenan yanzu.
Magajin garin ya ce: “A ranar Talata da safe an kira shugaban masu garkuwar har ma yana tambaya game da kuÉ—in fansa. Da aka nemi a yi magana da sarkin sai ya ce yana can yana jin É—umi a gefen wuta.
“Da aka yi magana da Kabiru ya tabbatar da cewa sarki na can yana jin É—umi, amma ya yi ta roĆ™on a biya kuÉ—in fansa domin kuÉ“utar da su.”
Wani ɗan sarkin na Gobir ya ce an yi wa mahaifin nasa kwanton-ɓauna ne a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa gida.
“‘Ćłan bindigar sun fara harbi kan mai uwa da wabi lokacin da suka hangi motar mahaifin namu, abin da kuma ya janyo fashewar tayoyin motar da karkatar da hankalin direbansa har ta kai ya tsaya,” in ji É—an s.arkin.
Majiyoyi daga Sabon Birni sun ce an yi garkuwa da ƙarin mutum biyar a yankin a ranar da aka sace sarkin.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj