Gwamnatin Nijeriya Ta Gindaya Sabon  Sharadi Ga Dalibai Masu Rubuta Jarrabawar JAMB

FB IMG 1724658543798

Daga Aminu Bala Madobi

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya bayyana cewa daga shekarar 2025, ba za a sake ba wa ‘yan kasa da shekaru 18 izinin shiga jarrabawar shiga jami’a ta JAMB ba.

Alfijir Labarai ta rawaito farfesa Mamman ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV ranar Lahadi a Abuja, inda ya jaddada cewa mafi karancin shekarun da ake bukata don shiga jami’a a Najeriya, bisa tsarin ilimin kasar, shi ne shekaru 18.

Farfesa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar baiwa dalibai ‘yan kasa da shekaru 18 damar shiga jarabawar JAMB a wannan shekara domin baiwa iyaye sanarwar gaba game da sauye-sauyen da za su fara aiki a shekara mai zuwa.

“Babu wani abu da ya canza, mafi karancin shekaru har yanzu shekaru 18 ne, abin da muka yi a taron JAMB shi ne ba da damar wannan shekara ta zama irin sanarwa ga iyaye, a bana hukumar JAMB za ta dauki dalibai ‘yan kasa da shekara 18. Amma daga shekara mai zuwa. , JAMB za ta bukaci duk wanda ke neman shiga jami’a a Najeriya ya cika shekaru 18 da ake bukata,” inji Farfesa Mamman.

Ya kuma kara da cewa, wannan ba sabuwar manufa ba ce, illa dai aiwatar da wata manufa ce. “Idan ka lissafta adadin shekarun da ya kamata dalibai su yi a makaranta—daga renon yara har zuwa makarantar firamare da sakandare—za ka cika shekaru 17 da rabi. A lokacin da dalibai suka shirya shiga, ya kamata su kai shekarun da suka dace. ” ya kara da cewa.

Bugu da kari, Ministan ya sanar da cewa daliban da ba su kammala mafi karancin shekarun da ake bukata a makaranta ba, ba za su iya shiga dukkan jarrabawar Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) da Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC).

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *