Shugaban Hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji, shine ya jagoranci kaddamar da kwamitocin a harabar hukumar.
Sheikh Daneji yace wadannan kwamitoci ana umartarsu da suyi aiki domin samar da wadannan kalandoji kamar yadda aka saba.
Kwamitin na samar da Kalanda yana karkashin Shugabancin, Sheikh Abbas Abubakar Daneji.
Sai Kwamitin Samar da Ayoyi da Maudu’ai wanda yake karkashin Kwamishina na 1 Gwani Hadi.
Sai kuma Kwamitin Samar da Hadisai da Hikimomi wanda yake karkashin jagorancin kwamishina na 2 Sheikh Ali Danabba.
Da kuma Kwamitin dubawa da tabbatarwa karkashin Jagorancin Kwamishina na 1 Gwani Hadi.
Haka zalika akwai kuma Kwamitin Nisabi wanda Sheikh Ibrahim Falaqi yake shugabanta.
Sai Kwamitin raba kalanda karkashin Shugabancin, Umar Sani Mukhtar.
Baya ga Kwamitin Samar da Kalandar an kuma kaddamar da Kwamitin Bada Shawarwari na Ma’aurata da kuma Na tsaftar Muhalli.
A karshe Sheikh Abbas Daneji Ya kuma ja hankalin dukkanin Shugabbani da Mambobinsu dasu tsaya suyi aikin yadda ya kamata domin wannan aikin Al’umma ne bana Hukumar Shari’a Commission Ba.
Taron Kaddamarwar ya samu halartar kwamishinonin Hukumar Gwani Hadi da kuma Sheikh Ali Danabba da Daraktoci da Sauran Mambobin Hukumar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD