Wasanni: Ahmad Musa ya yi ritaya daga Super Eagles bayan shekaru 15 yana buga kwallo

FB IMG 1765987437973

Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga buga wasan ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa da ƙasa, inda ya kawo ƙarshen shekaru 15 da ya shafe yana wakiltar Super Eagles, tarihin da ya sa ya zama ɗan wasan Najeriya mafi yawan bugawa da kuma ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasa na zamani, kamar yadda jaridar PUNCH Online ta rawaito.

Musa ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta a yammacin ranar Laraba, inda ya waiwayi tafiyarsa tare da bayyana alfaharin wakiltar ƙasarsa.

“Bayan dogon tunani, na yanke shawarar yin ritaya daga buga wasan ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa da ƙasa, tare da kawo ƙarshen kusan shekaru 15 da na shafe ina buga wa Super Eagles,” in ji shi.

“Tun daga kiran farko da aka yi mini, sanya rigar kore da fari na Najeriya na kasancewa babban abin alfahari a gare ni.”

Musa ya kuma jaddada girman darajar da ya kai har zuwa  wasanni 111 da ya bugawa Najeriya.

“Buga wasanni 111 wa ƙasata abu ne da nake girmamawa ƙwarai. Zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan bugawa a tarihin ƙwallon ƙafar Najeriya babban abin ɗaukaka ne. Duk lokacin da na saka riga, na fahimci nauyin alhakin da ke tare da ita.”

Musa na daga cikin ‘yan wasan da suka lashe Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na 2013, sannan ya kafa tarihi a matsayin ɗan Najeriya na farko da ya ci ƙwallaye fiye da ɗaya a wasa guda na Kofin Duniya, lokacin da ya zura wa Argentina kwallaye a gasar 2014. Daga baya kuma ya zama ɗan Najeriya na farko da ya ci ƙwallaye a Kofin Duniya guda biyu, inda ya zura kwallaye biyu a ragar Iceland a gasar 2018. Ya ce waɗannan lokuta abubuwa ne da ba zai taɓa mantawa da su ba.

For advertisement or further advisory services, the public has been directed to contact +2348032077835.

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news Fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *