Manta Sabo: Kotu a Kano ta daure wani tsoho mai shekara 85 shekaru 14 kan laifin fyade

FB IMG 1760790928482

Wata kotu a Jihar Kano  da ke zamanta a Gwarzo ta yanke wa wani dattijo mai shekara 85, Malam Isah, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa laifin yi wa wata karamar yarinya fyade.

Kotun ta bayyana cewa an aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, a kauyen Sauna da ke karamar hukumar Gabasawa a jihar.

Yayin yanke hukunci, Mai shari’a Aisha Mahmoud ta ce bangaren masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, bayan gabatar da hujjoji masu gamsarwa a gaban kotu.

Bisa haka, kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Da yake mayar da martani, Kwamishinan Shari’a na jihar kuma Babban Lauyan Jiha, Abdulkareem Kabir Maude, ya yabawa tawagar masu gabatar da kara bisa kokarinsu da jajircewa wajen gudanar da shari’ar.

Ya kuma jaddada kudurin ma’aikatar shari’a na tabbatar da an yi adalci a dukkan lamura, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta sassauta wajen hukunta masu aikata irin wadannan laifuka ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *