Atiku Alama Ce Ta Hidima, Sadaukarwa Ga Al’umma – Shugaba Buhari

Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi kan hidima da sadaukar da kai.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake taya Atiku murnar cika shekaru 61 da haihuwa.

Shugaban ya bayyana gwamnan a matsayin shugaba mai kwazo da sadaukar da kai.

Buhari ya ce shugaban kungiyar gwamnonin masu ci gaba a kodayaushe yana gudanar da ayyukansa ne da kwazon haiki, da kirkire-kirkire mara misaltuwa.

A cikin sakon taya murna ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, Buhari ya ce: “Allah ya ba ka karfi da lafiya don cimma dukkan manufofinka.”

Haka kuma, Buhari ya taya gwamnan jihar Oyo Oluseyi Makinde murnar cika shekaru 55 da haihuwa.

Buhari ya ce Makinde dan siyasa ne mai hangen nesa mai kishin ci gaban Najeriya.

“Ina yi masa murnar zagayowar ranar haihuwa, kuma ina rokon Allah Ya ba shi lafiya da tsawon rai,” in ji Buhari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *