Alfijr ta rawaito Rundunar EFCC shiyar jihar Lagos ta gurfanar da mawallafin kamfanin Macmillan Najeriya tare da Farfesa Adesanya Iyiola Adelekan da Bola Fasasi a gaban mai shari’a Mojisola Dada na kotun laifuffuka ta musamman da ke zaune a Ikeja, Legas, bisa zargin damfarar $922m.
An gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu, 2023, kan tuhume-tuhume shida da suka shafi hada baki da kuma karbar ta hanyar karya da ya kai dalar Amurka miliyan 922 (Dalar Amurka miliyan dari tara da ashirin da biyu).
Macmillan Nigeria Publishers, Farfesa Adesanya lyiola Adelekan da Bola Fasasi, a wani lokaci a shekarar 2018, sun samu littafai na siyarwa da suka kai dalar Amurka $226,900.00 ta hanyar karya, daga BHS Book Printing SD BHD na Selangor Malaysia bisa zargin cewa za su sayar da littattafan su mika kudin.
Daga tallace-tallacen da aka yi a cikin makonni biyu da samun takardar biyan kuÉ—i, wanda ke nuna cewa sun san ko ya kamata su san karya ne, kuma sun aikata laifin samun kaya ta hanyar karya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇