Alhassan Doguwa ya samu lambar yabo bisa biyawa ɗalibai kudin Makaranta

FB IMG 1696340580978

Dan majalisa Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Tudun wada da Doguwa a Majalissar Kasa Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya shawarci masu hannu da shuni da shugabanni da su Tallafawa Ilimi ta ko wacce fuska domin cigaban kasa.

Alfijir Labarai ta rawaito Hon Doguwa na wannan bayani ne a lokacin da shugabannnin kungiyar Daliban kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa suka bashi lambar yabo bisa irin tallafin kudin makaranta da ya biya ga ɗaliban yankin da ke karatu a Jami, oin kasannan.

Doguwa yace zasu cigaba da baiwa ɗaliban yankin gudunmawa domin matasan yankin su cigaba da yin fice a fannoni na rayuwa.

Da suke jawabin shugabannin kungiyoyin ɗaliban kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa kwamared
Isma,il Hashim Tudun wada da kwamared Abduljalal Umar, sun bada lambar yabo ne ga Alhassan Ado Doguwa a matsayinsa na mutumin da yasan darajar da mahimmancin ilimin Addini dana zamani.

Don haka ne yake samun lambar yabo ta ko wanne fanni musamman bangaren ILIMI.

Kungiyoyin ɗaliban sun sha Alwashin cigaba da bada gudunmawa da wayarda Kan matasa maza da mata bisa dubban ayyukan alheri da Doguwa ya ke gudanarwa a yankunan kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa.

Kamar yadda kakakinsa Auwal Sufi ya aikowa jaridar Alfijir Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *