Amnesty International tayi gagarumin taro da manyan yan jaridu a kan kare hakkin al’ummar Kano

FB IMG 1700314764894

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Najeriya ta gudanar da taron manema labarai da masu fafutuka da kungiyoyin kare hakkin dan adam a Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito an gudanar da taron ne domin tattaunawa kan hadin gwiwa don tattara bayanai, kariya da kuma kiyaye haƙƙin ɗan adam.

Jaridar Alfijir Labarai na daya daga cikin jaridar yanar gizo da aka gayyata, bayan malaman jami a da sauran yan gwagwarmaya

Taron ya kuma tattauna sabbin dabaru da sabbin hanyoyin magance cin zarafin jami an tsaro, da suka shafi jinsi, ‘yancin yara, tare da kai hari akan al’ummar da basu ji basu gani ba, da kuma yunkurin dakile ‘yancin fadin albarkacin baki.

Amnesty International ta baje kolin ayyukanta a Najeriya da abubuwan da suka fi ba da fifiko da suka hada da rikice-rikice, yaki da wariyar launi, da kuma hakkin dan adam.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

2 Replies to “Amnesty International tayi gagarumin taro da manyan yan jaridu a kan kare hakkin al’ummar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *