An Ɗauke CP Na Kano Bayan NNPP Ta Yi Ƙorafin Ya Kama Mambobinta

Alfijr ta rawaito Kwana ɗaya bayan da jam’iyyar adawa ta NNPP ta yi kira da a ɗauke kwamishinan Ƴan Sanda na jihar Kano, Mamman Dauda, ​​bisa zargin nuna son kai, Sifeto-Janar na Ƙasa, Alkali Baba, ya maida shi jihar Plateau domin gudanar da zabe.

A jiya Lahadi ne jam’iyyar NNPP ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, domin nuna adawa da kamawa da tsare wasu manyan mambobinta sama da 100 da kwamishinan ya yi.

Sai dai kuma a wata sigina da DAILY NIGERIAN ta samu, Sifeto-Janar din ya mika Dauda zuwa Plateau, sannan ya tura CP Mohammed Yakubu zuwa Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, IGP din ya kuma tura manyan jami’an ‘yansanda zuwa kowane gundumomi 109 na ‘yan majalisar dattawan kasar nan a lokacin zabe.

A wani sabon sako da aka fitar bayan soke na baya ba zato ba tsammani, IGP ya tura CP Ita Uku-Udom zuwa gundumar Kano ta tsakiya; CP Sunday Babaji mai zuwa mazabar Kano ta kudu da DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano ta Arewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

2 Replies to “An Ɗauke CP Na Kano Bayan NNPP Ta Yi Ƙorafin Ya Kama Mambobinta

  1. To a gaskiya munyi murna da abinda IGP yayi Dan Samar da zaman lafiya da ingantaccen zabe a jihar Kano. Allah ya zaba mana wadanda zasu ji tausayinmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *