An bukaci Ganduje ya gayawa Tinubu gaskiyar halin da Najeriya ke ciki

FB IMG 1703242586089

Wani tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, ya bukaci shugaban jam’iyyar APC, Umar Ganduje, ya sanar da shugaba Bola Tinubu game da hakikanin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.

Alfijir labarai ta rawaito Fayemi ya ce kamata ya yi Ganduje ya bai wa Tinubu gaskiyar zancei daga al’umma don kada shugaban kasa ya dogara da abin da yake ji a “Villa da ya kulle.”

Tsohon gwamnan ya yi magana ne a ranar Talata a wajen wani taron ƙaddamar da littafi mai suna: ‘APC & Transition Politics’, wanda wani jigo a jam’iyyar APC, Salihu Lukman ya rubuta.

Ya kuma bukaci jam’iyya mai mulki da ta cika takardar ta, kuma kada ta zama ‘yar kallo’ wajen tsara manufofi.

Tsohon gwamnan ya koka da yadda mawakan siyasar suka sa wadanda ke fadar shugaban kasa ke da wuya su san hakikanin halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

A cewar Fayemi: “Na yi farin ciki da shugabanmu ya zo nan. Wannan ita ce jam’iyyar da bai kamata ta zama ‘yar kallo ba wajen tsara manufofi.

“Ya kamata wannan jam’iyya ta zama ita ce za ta tsara tsarin jam’iyyar.

“Ya kamata wannan jam’iyyar ta kasance ita ce ta gaya wa shugaban kasa cewa wannan ra’ayi ne daga al’umma da mazabu da ke can, ba wai abin da yake ji a Villa da aka kulle shi ba.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *