An dakatar da likitan da ya naushi mara lafiya yana tsaka da yi mata tiyata

FB IMG 1703255434528

Hukumomin China suna gudanar da bincike a wani asibiti inda aka samu wani likita da ake zargi da naushin mara lafiyar da yake tsaka da yi wa tiyata.

Alfijir labarai ta rawaito anga lamarin ne cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a China, lamarin da ya fusata al’ummar ƙasar.

Asibitin na Aier China ya dakatar da likitan tare da korar shugaban asibitin da lamarin ya faru a 2019.

BBC ta tuntuɓi asibitin domin jin ta bakinsu.

Bidiyon ya nuna yadda likitan yake naushin mara lafiyar a ka sau uku yayin da yake tiyata a idonsa.

Aeir China da ke tafiyar da asibitocin ido da dama, ya ce lamarin ya faru ne lokacin wata tiyata a asibitinsa da ke Guigang a kudu maso yammacin China.

Mara lafiyar mace ce ƴar shekara 82 kuma yayin tiyatar saboda allurar kashe zafi da aka yi mata, ta sa a lokuta da dama ta yi ta motsa kanta da kuma ƙwayar idonta, kamar yadda wata sanarwa daga asibitin ta bayyana.

Hukumomi a yankin sun ce mara lafiyar ta ji rauni a goshinta. Kuma ba ta jin wani yaren sai na garinsu sannan ba ta gane gargaɗin da likitan yake mata ba a harshen Mandarin, lamarin da ya sa likitan ya yi yadda yake so da ita a lokacin gaggawa.

Bayan tiyatar, asibitin ya nemi afuwa tare da biyan yuan 500 – kwatankwacin dala 70 a matsayin diyya, a cewar ɗan matar wanda ya yi wa kafafen yaɗa labaran ƙasar bayani.

Ya kuma ce mahaifiyarsa a yanzu ba ta gani da idonta na hagu, sai dai babu tabbacin ko hakan ya faru ne saboda lamarin da ya faru.

A jiya Alhamis ne aka sanar da korar shugaban asibitin na Guiyang da kuma dakatar da likitan – wanda shi ma babban jami’i ne a asibitin saboda take ƙa’idojin aiki.

Duk da lamarin ya faru a Disambar 2019, batun ya fito fili ne a wannan makon bayan fitacciyar likita a China, Ai Fen ta wallafa bidiyon tiyatar da na’urar CCTV ta naɗa.

Dr Ai, wadda ke cikin tawagar likitocin da suka ankarar da jama’a kan ɓarkewar cutar korona a Wuhan, ta wallafa bidiyon a shafinta na Weibo inda mabiya sama da miliyan biyu suka kalla.

BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *