Ba komai a jawabin Shugaba Tinubu, daga izgilanci sai rufa-rufa ga ‘yan Najeriya – LP

IMG 20240104 084457

Jam’iyyar ‘yan adawa ta LP ta bayyana jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya a safiyar sabuwar shekarar 2024 cewa babu komai a ciki, daga izgilanci sai rufa-rufa sai kuma shashantar da ‘yan Najeriya.

Alfijir labarai ta rawaito LP ta bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Litinin, wadda Sakataren Yaɗa Labaran LP, Obiora Ifoh ya sa wa hannu.

A cikin jawabin Tinubu, ya sake maimaita cewa ya ƙudiri aniyar cika dukkan alƙawurran da ya ɗaukar wa ‘yan Najeriya.

Ya kuma yi kira ga masu adawa da su matsa kusa da shi domin su yi aiki tare, tunda dai zaɓe ya wuce.

A martanin da LP ta yi wa Tinubu, ta ce jam’iyyar kamar sauran ‘yan Najeriya, ta na kallon jawabin babu komai a ciki sai harbin iska kawai.

Ta ce jawabin cike ya ke da rufa-rufa, yaudara da kuma rashin tausayin talakawan Najeriya.

“Saboda tsananin latsi da Shugaban Ƙasa ya yi, jawabin na sa kwata-kwata bai nuna jaje ko ta’aziyya ga iyalan mutum sama da 200 da aka kashe a ranar Jajibirin Kirsimeti a Jihar Filato ba. Wannan babban abin kunya ne.”

LP ta kuma zargi Tinubu da yin wasareren kasa taɓuka abin kirki wajen shawo kan manyan matsalolin da suka haɗa da tsaro, matattun masana’antu, tsadar rayuwa da tsadar kayan masarufi da kuma lalacewar martaba da darajar Naira.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa Tinubu bai ce komai ba dangane da zargin ƙazamar satar da manyan jami’an gwamnati ke ɗibgawa a ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban.

Sannan kuma LP ta ragargaji Tinubu dangane da gaggawar cire tallafin
fetur da ya yi ba tare da shawara ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *