Wata dalibar Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Mubi, Jihar Adamawa ta kashe kanta sakamakon rabuwa da saurayinta.
Dalibar mai shekara 24 tana karatun aikin jarida ne a Kwalejin kuma tana aikin daukar horo ne a gidan talabijin na Adamawa (ATV) da ke Yola.
Alfijir labarai ta rawaito Dalibar wacce ’yar asalin Garkida Gombi ce, an tsinci gawarta ne a dakinta da ke unguwar Hayin Gada, a Karamar Hukumar Girei a jihar.
Ana zargin ta sha guba ne sakamakon bakin cikin rabuwa da saurayinta.
Rahotanni sun bayyana cewa, saurayin Balami wanda malami ne a Jami’ar Maddibo Adama (MAU) ya bukaci su rabu, lamarin da ake ya sanya ta kashe kanta.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce mahaifin dalibar ya kawo musu kara kan lamarin.
Kakakin ya ce rundunar za ta yi bincike domin gano musabbabin mutuwar dalibar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V