Babu hujjar da ke nuna cewa takardun digirin Tinubu na bogi ne – In Ji BBC

Screenshot 20231005 110321 com.android.chrome edit 3478762294779

Babu wata hujja da ke nuna cewa takardun karatun digiri da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa hukumar zaɓen ƙasar na bogi ne, kamar yadda Ayarin BBC Mai Tantance Labaran Karya a Duniya ya gano.

Zarge-zargen cewa takadar kammala karatun digirin shugaba ta jabu ce, ya cika shafukan sada zumunta, bayan Jami’ar Jihar Chicago (CSU) ta fitar da bayanan karatunsa a makon jiya.

Mun duba wasu daga cikin zarge-zargen da aka fi yaɗawa a shafukan sada zumunta.

Fitar da takardun karatun shugaban ƙasar shi ne ƙololuwa a batun ƙarar da ɗaya daga cikin manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya shigar a watan Agusta.

Atiku dai ya yi fatan za a soke cancantar wanda ya yi nasara a zaɓen, bayan ya zarge shi da yin jabun takardar karatunsa ta digiri kan nazarin harkokin kasuwanci a Jami’ar Jihar Chicago cikin 1979, wadda ya miƙa wa hukumar zaɓe ta Najeriya.

A ƙoƙarinsa na samun shaida kan ƙarar da ya shigar a Najeriya, Atiku Abubakar ya garzaya wata kotun Amurka a watan Agusta, inda ya buƙaci ta tilasta wa Jami’ar CSU ta fitar da bayanai game da takardun karatun Tinubu, bisa wani tsari da ake kira ganowa, inda ɓangarorin da ke cikin magana, ke musayar bayanai a ciki har da muhimman bayanan takardu kafin fara shari’a.

Lauyoyin Tinubu dai sun ƙi amincewa da wannan buƙata, saboda dalilai na kare sirri, amma kotun Amurka ta yanke shawarar cewa ana iya ci gaba.

Takardun da Atiku Abubakar ya buƙaci a fito da su su ne:

Kwafin duk wata digiri da Jami’ar CSU ta bayar a 1979.

Kwafin shaidar karatu da CSU ta bai wa Tinubu a 1979.

Kwafin digiri mai tsarin rubutu iri ɗaya da hatimi da sa hannu da kuma kalmomi iri ɗaya ga sauran ɗalibai waɗanda suka yi daidai da abin da jami’ar ta bai wa Tinubu a 1979.

Takardun bayanai daga CSU wanda wani jami’in jami’ar Jamar Orr ya tabbatar, a cikin watanni 12 daga ranar 1 ga watan Agustan 2022

Dangane da buƙatar farko, jami’ar ta gabatar da takardun digiri guda bakwai da suka ƙunshi fannoni daban-daban tare da sunayen ɗaliban da aka tantance.

A cewar magatakardan jami’ar, ɗaliban ba su karɓi takardun kammala digiri ba.

Da take mayar da martani ga buƙata ta biyu, jami’ar ta bayyana cewa ba za ta iya samun takardar digiri da ta bai wa Tinubu a 1979 ba, saboda ba sa ajiye kwafin takardun da ɗalibai suka riga suka karɓa.

A buƙata ta uku kuma, jami’ar ta bayyana cewa, ta bai wa Tinubu madadin takardar digiri mai ɗauke da kwanan wata 27 ga watan Yuni 1979.

Ta kuma fitar da shaidar karatun digiri da aka bai wa sauran ɗalibai mai tsarin rubutu iri ɗaya da hatimi da kuma sa hannu da kalmomi iri ɗaya, a matsayin takardar Tinubu.

Dangane da buƙata ta huɗu, jami’ar ta miƙa wasu takardun karatu waɗanda tun farko Mista Jamar Orr ya tabbatar sannan ya fitar da su.

Atiku Abubakar wanda shi ne ya zo na biyu, yana ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Bisa hukuncin da alƙali ya yanke, lauyar Atiku Abubakar, Angela Liu, a makon jiya, ta yi wa Caleb Westberg, magatakardan Jami’ar Jihar Chicago na yanzu, tambayoyi, bayan ya yi rantsuwa zai bayar da bahasi na gaskiya a kotu.

Mai magana da yawun Atiku Abubakar Phrank Shaibu ya bai wa BBC damar ganin takardun bahasin rantsuwar kotun.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya sun yi zargin cewa bahasin kotu da takardun digiri da Jami’ar Jihar Chicago ta fitar, sun tabbatar cewa takardar digirin da Tinubu ya miƙa wa hukumar zaɓe, na bogi ne.

Wannan iƙirari ne, Kalu Kalu ɗaya daga cikin lauyoyin Atiku Abubakar, shi ma ya sake maimaitawa a wani taron manema labarai cikin makon jiya.

Mun gano cewa babu wata shaida da ke tabbatar da wannan iƙirarin.

Yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya suna ta yaɗa labaran ƙarya game da bahasin kotu da Caleb Westberg, magatakardar CSU na yanzu ya bayar

Jami’ar Jihar Chicago ta fitar da takardu masu yawa na kammala digiri daga 1979 zuwa 2003.

Mun yi duban tsanaki a kan dukkaninsu.

Akwai takardun digiri daban-daban guda uku na Tinubu da muka yi nazari kansu a ɗaukacin binciken da muka yi:

Daya ta ainihi, daga 1979, wadda a baya ya ce ta ɓata lokacin da ya tafi neman mafaka a shekarun 1990.

Ta biyu, wadda ya gabatar wa INEC – kuma ake ƙaddarawa madadin digirin Jami’ar Jihar Chicago (iri ɗaya da takardun digirin da Jami’ar Jihar Chicago ke bayarwa a shekarun 1990).

Bugu da ƙari, Jami’ar Jihar Chicago ta riƙe wata takardar shaidar digiri ta Bola Tinubu, wadda suka ce mai yiwuwa ya yi a farkon shekarun 2000, amma bai karɓa ba

Zarge-zargen da ake yi a shafukan sada zumunta sun dogara ne a kan kwatanta takardun karatun da Bola Tinubu ya gabatar wa INEC da kuma takardar digirin 1979 da Jami’ar CSU ta fitar.

A bahasin gaban kotu da Caleb Westberg ya bayar, mayar da hankali ne a kan kwafin takardar da Shugaba Tinubu ya gabatar wa hukumar zaɓe, inda ya nuna cewa babu yiwuwar tana ɗaya daga cikin takardun digiri da Jami’ar CSU ta fitar.

Sai dai, ko da yake Mista Westberg ya yarda da Misis Liu cewa takardar digirin da ake magana a kai, ba ta yi kama da kwafin takardun digirin Tinubu na 1979 ba, amma ya ce haƙiƙa shaidar karatun ta yi kama da ɗaya daga cikin takardun digiri guda uku da Jami’ar CSU ta fitar ga Atiku Abubakar.

Bincikenmu ma ya tabbatar da haka.

Ya bayyana cewa bambance-bambancen da aka samu a tsarin takardar digirin sun faru ne, saboda takardar, an sake fitar da ita ne a shekarun 1990.

Caleb Wetberg ya ce fasalin takardar digirin Jami’ar CSU ya canza a karo da yawa tsawon shekaru.

Ya ce duk wata buƙatar takardar digiri da aka gabatarwa jami’ar, za ta yi kama ne da fasalin takardun digiri da jami’ar ke bayarwa na lokacin ne, ba tare da la’akari da lokacin da ɗalibi ya kammala karatu ba.

A kan haka, lokacin da Bola Tinubu ya sake neman takardar digirinsa a ƙarshen shekarun 1990, abin da za a ba shi, zai yi kama ne abin da jami’ar ke fitarwa ne a wancan lokaci ne.

Takardar kammala karatun digiri

Takardar digiri ta CSU da aka bai wa ɗalibai a 1998 da 1999. Na shekarar 1998 sun yi daidai da takardar digiri da Tinubu ya miƙa wa hukumar zaɓen Najeriya.

Takardun digiri guda uku na shekarun 1990 da Jami’ar CSU ta fitar sun yi kama da na Tinubu.

Daya daga cikinsu, wadda ke ɗauke da kwanan watan 18 ga watan Disamban 1998, iri ɗaya ce (ban da suna da matsayin digiri da kwanan wata), da takardar shaidar digirin da Bola Tinubu ya gabatar wa hukumar zaɓe.

Caleb Westberg ya kuma ce Jami’ar CSU ba ta ajiye rubutaccen bayani a duk lokacin da wani tsohon ɗalibi ya nemi ta sake ba shi kwafin takardar digiri, don haka ba a ajiye bayani a kan bukatar da Bola Tinubu ya gabatar ta neman kwafin shaidar digiri ba.

Bahasin shaidar Westberg

Westberg ya faɗa wa lauyar Atiku, Angela Liu, cewa Jami’ar CSU ba ta tara bayanan buƙatun da ɗalibai suka nema na sake karɓar shaidar kammala karatu.

Kwafin da Tinubu ya bai wa hukumar zaɓe, akwai wani ɓangare da ya ɓata na tambarin jami’ar, wadda Westberg ya ce faɗa a bahasin shaidarsa cewa mai yiwuwa “an yanke” ne a lokacin da ake kwafin shi.

Mun yi nazari kan takardun digirin kuma ga dukkan alamu a zahiri ba a haɗa da ɓangaren ƙasan takardar ba a wajen buga kwafin.

Wannan ne takardar digiri ɗin da  Tinubu ya mika wa hukumar zaɓen Najeriya – da’irar launin ja ta bayyana bangaren da babu.

Wannan ce takardar digiri da Tinubu ya miƙa wa hukumar zaɓen Najeriya – da’irar launin ja, ta bayyana ɓangaren da babu.

BBC dai ta tuntubi jami’an Tinubu domin samun kwafin takardar digirin da ake magana a kai.

Sai suka aiko wadda suka ce ita ce kawai kwafin takardar kammala karatunsa da ta rage.

Kwafin takarda ne da aka buga mai rubutu baƙi da fari, wadda irin ɗaya ce da abin da ya kaiwa INEC.

Wani iƙirarin kuma, da wata cibiyar binciko gaskiyar lamari a Najeriya ta yi, shi ne digirin da Bola Tinubu ya gabatar, ba daga Jami’ar CSU ta fito ba, saboda shaidar digirin jami’ar ba ya ƙunsar kalmomin “with honors” (da ƙarin daraja) a ƙarƙashin matsayin digiri da ɗalibi ya samu.

Sai dai, BBC ta gano cewa ko da yake ba a nuna hakan a kan sauran takardun digirin da Jami’ar CSU ta fitar ba, amma an ga kalmomin a shaidar karatun digirin Tinubu da mai yiwuwa aka ba shi a farkon shekarun 2000, wadda Caleb Westberg ya tabbatar da sahihancinta a lokacin da yake ba da bahasi a kotu.

Tana ɗauke da kalmomin “da ƙarin daraja” – abin da ya yi daidai da shaidar digiri mai irin waɗannan bayanai kamar yadda shugaban ƙasar ya miƙa wa hukumar INEC.

Har yanzu takardar digirin Tinubu tana hannun jami’ar CSU, bai karɓa ba

Magatakardan Jami’ar CSU, ya ce makarantarsu tana iya tabbatar da sahihancin wannan takardar digiri, saboda har yanzu tana nan a hannu, ba a karɓe ta ba.

Ba kowanne ɗalibi ne yake kammala digiri a jami’ar da ƙarin daraja ba. Bola Tinubu kamar yadda Jami’ar CSU ta ba da shaida a takardun kotu da dama da BBC ta gani, ba shakka ya kammala jami’ar CSU, da digiri mai ƙarin daraja.

BBC ta tuntuɓi jami’ar CSU game da wasu tambayoyi a kan takardun digirinsu kuma sun yi mana nuni ga wani bayani wanda a wani ɓangare ke cewa: “Muna da ƙwarin gwiwa kuma ko yaushe muna tantance gaskiya da ƙimar bayanan da muke ajiyewa a kan karatun digirin Tinubu, da kuma sharuɗɗan kammala karatunsa”.

Wani zargi da ya cika gari a shafukan sada zumunta shi ne mutumin da ya halarci jami’ar CSU da sunan Bola A Tinubu, mace ce.

Bola Tinubu ya halarci Kwalejin Southwest (wadda a yanzu ake kira da Richard J. Daley College) kafin ya tafi Jami’ar CSU a 1976.

A takardar shaidar Kwalejin Southwest akwai harafin “F” (da ke nufin “mace”) a gurbin da ake nuna shaidar jinsin mutum, lamarin da ya janyo jerin iƙirari iri daban-daban cewa mace ce ta halarci makarantar, kuma Bola Tinubu “ya saci bayananta”.

Lauyan Atiku, Mista Kalu ya yi nuni da haka, a lokacin wani taron manema labarai cikin makon jiya.

Sai dai a bahasin shaidar da ya gabatar, Caleb Westberg ya jaddada cewa babu ruɗani game da jinsin mutumin da ya halarci jami’arsu ta CSU, don kuwa namiji ne mai suna Bola A Tinubu.

Ya ce jami’ar tana amfani da wasu hanyoyi, ba kawai suna ba, wajen tabbatar da sahihancin bayanan kowanne ɗalibi.

A cewarsa, lambar shaida ‘yan ƙasa da mazauna Amurka (SSN) da ke jikin takardar karatu ta Kwalejin Southwest ta yi kama da wadda suke da ita a sauran takardu, waɗanda kuma sun fayyace jinsin ɗalibin ƙarara, cewa namiji ne.

Takardun da aka fitar, sun kuma bijiro da tambayoyi game da ranar haihuwar Tinubu da makarantar sakandire da ya halarta.

Daya daga cikin takardun ta bayyana cewa Bola Tinubu ya halarci sakandiren Government College Lagos a 1970. Sai dai bayanan da ke shafin intanet na makarantar sun zayyana cewa an kafa ta ne a 1974.

Baya ga bambance-bambance a kan jinsi da ranar haihuwa a wasu takardu da aka fitar, da suka sha bamban da ranar haihuwar Shugaba Tinubu a hukumance ta 29 ga watan Maris 1952.

Takardar karatunsa daga Jami’ar CSU na ɗauke da ranar haihuwa ta 29 ga watan Maris 1954. Takardarsa ta neman shiga jami’a na ɗauke da ranar haihuwar 29 ga watan Maris 1955.

Lauyan Atiku Abubakar ya ce a lokacin da Caleb Westberg yake bayar da bahasi a kotu cewa, takardun da Tinubu ya miƙa wa hukumar zaɓe, sun nuna 29 ga watan Maris 1952 a matsayin ranar haihuwarsa.

Kuma lokacin da Caleb Westberg yake amsa tambayoyi a kotu, ya ba da amsa da cewa waɗannan bambance-bambance, tana iya yiwuwa sun faru ne saboda ajizancin ɗan’adam.

Mun tuntuɓi jami’an Bola Tinubu game da waɗannan bambance-bambance kuma wani mai magana da yawunsa ya nemi mu je ga jam’iyyarsa – ta APC.

Daga nan sai muka tuntuɓi mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaben Tinubu, Festus Keyamo, wanda kuma minista ne a gwamnatin Najeriya.

Bai amsa kiraye-kirayenmu ko mayar da amsa ga saƙonnin waya da na whatsapp da muka aika masa ba. Mun kuma aika tambayoyi ga jami’an Atiku Abubakar. Su ma, ba su bayar da amsa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *