Badala: Ɗalibai Mata Sun Yi Zanga-Zanga Kan A Kori Shugaban Sashin Shari’a

Tarin dalibai mata ne na Jami’ar Jihar Calabar suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da halin dan bunsuru da wani malamin sashen koyon aikin sharia ke yi musu mai suna Farfesa Cyrill Ndifon.

Alfijir Labarai ta rawaito a yammacin ranar Lahadi ne matan suka yi tururuwa suna furta kalaman “Dole a kori Ndifon” mun gaji da abinda kake mana, Daliban bangaren Shari’a ba abun banza bane.

Shi ma shugaban daliban ɓangaren Shari’a na Jami’ar Kwamared Benedict Otu ba a barshi a baya ba wajen bin sahun ɗalibai matan don gudanar da zanga-zangar.

Da yake maida martani ta wayan tarho game da lamarin, Farfesa Ndifon ya musanta zarge-zargen da mata suka masa musamman ga batun cin zarafi ta hanyar lalata.

Kuma ya bayyana cewa ita kanta zanga-zangar ma wata manaƙisa ce daga wasu masu kokarin ganin bayansa a Jami’ar.

Ya ƙara da cewa wadannan zarge-zarge an yi su ne kurum don shafa masa kashin kaji.

“An yi ta shirya mun gadar zare a Jami’arnan tun bayan da na kada wasu mutane a zaɓen da aka yi, toh amma cikin ikon Allah ina tsallakewa”

“Waɗannan zarge-zarge zancen banza ne zancen wofi waɗanda wasu suka kitsa da manufar sai sun ga bayana a Jami’ar kasancewar ina nasara sau biyu a jere a matsayin shugaban tsangayar koyon aikin Shari’a ”

Da yake magana kuma dangane da rubutun dake ɗauke a jikin kwalayen, Farfesa Ndifon ya ce wani mutum guda ke da alhanki wannan maƙisa.

“Idan ka lura da rubutun, za ka ga dukkansu rubutun mutum guda ne. Sannan indai ba maƙisa ba ce ya aka yi ɗaliban suka san muna da ganawa da shugaban Jami’ar indai babu hannun wani algungumi”?

“Muna ƙoƙarin ganawa da shugaban Jami’ar kan wasu matsaloli dake ci mana tuwo a ƙwarya a wannan tsangaya, kwatsam sai muka ji wai ga ɗalibai suna zanga-zangar a koreni”

A hannu guda Farfesan ya zargi shugaban ɗaliban da hannu wajen tara matan da su yi dandazo zuwa dandalin taron don shafa masa kashin kaji.

“Wannan ƙarairayi nasu ba za su yi tasiri ba, da ma akwai wasu abokan aikina da suka sha alwashin ganin bayana.

Abin tambaya a nan shine, ina matan da suka ce ina lalata da su din”

Tuni dai shugaban Jami’ar Farfesa Florence Obi ya sha alwashin yiwa wannan tufka hanci ta hanyar lalama.

Premium Times Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *