Bashir Ojulari: Me yasa ake tsoron gaskiya ta yi aiki a NNPC?

IMG 20250808 WA0620

Daga ABDULLAHI MOHAMMED

A duniyar siyasa da harkokin mulki, kasuwar shakku da jita-jita ne suka fi ci, yayin da labaran ƙarya su kan zama makaman yaga mutuncin abokan hamayya.

A kwanakin nan, sunan Bashir Bayo Ojulari, Babban Darakta kuma Shugaban Hukumar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), ya shiga sahun waɗanda ake yawan ambato da jita-jita marasa tushe akansu.

Rahoton da gidan jaridar TheCable ta fitar da’awar “na musamman” ba ya da kamannin bincike na gaskiya, illa dai tamkar hukunci da aka dora masa kwalliya ta aikin jarida ne.

A cikin sakonsa, rahoton kokarin nuna cewa, kwanakinsa a ofis sun kare, saboda alakar aiki da ya yi da Abdullahi Bashir-Haske, wani mai kamfani da ke da alaka da dan tsohon mataimakin shugaban kasa.

Amma idan aka dubi lamarin da idon adalci, babu wani laifi da aka tabbatar da Ojulari ya aikata, kuma babu dokar da ya karya.

Wannan irin jita-jitar tana kokarin zana shi da kwatankwacin “madaukakin mai cin amana,” saboda kawai ya yi hulda da wani mai kamfani wanda matarsa ’yar wani fitaccen dan siyasa ce.

A wannan kasar da kowa ke da alaka da wani, ko dai yan uwa ne, makwabci, abokin makaranta ko kuma tsohon abokin aiki, za mu rushe tushen ci gaban kasa idan har muka fara ganin dangantakar dangi a matsayin laifi.

Ojulari bai hau kujerar shugabancin NNPC don ya yi wa wata kungiya biyayya ba, ko don ya raira wa wata jam’iyya waka ba. An zabe shi ne saboda kwarewarsa da fahimtarsa tsakanin fasahar duniya da tsarin cikin gida.

Tun lokacin da ya hau kujerar, ya kawo sabbin hanyoyin aiki da suka maye gurbin kazamin tsohon tsarin da ya dogara da son zuciya da ’yan fassara.

Ya karbi ragamar NNPC a wani lokaci mai sarkakiya, bayan aiwatar da Petroleum Industry Act, bayan komawar NNPC kamfani, kuma bayan juyin ra’ayi na yarda da kamfanin daga al’umma.

Amma maimakon ya tsaya don ya yi kallo, ya fuskanci tsofaffin matsaloli kai tsaye: ya fara bincike, rage almubazzaranci, ya sake fasalin tsarin aiki, kuma ya janyo gwiwar jama’a wajen ganin NNPC ta tashi daga duhu zuwa gaskiya.

Duk da haka, wannan gyara ya shiga kunnen wadanda suka dogara da tsohon tsarin na almubazzaranci da cin hanci. Su ne wadanda ke ta fitar da kagaggun labarai da nufin jefa Ojulari cikin rudani.

Amma kamar yadda fitaccen dan falsafa Plato ya ce, a tatsuniyarsa ta kogon duhu, wadanda ke cikin duhu sukankii wanda ya fita ya ga haske. Ojulari, da alama, ya zama irin wannan mutum da ya dauki haske, wanda wasu ke qoqarin dawo da shi cikin duhu.

Idan da gaske ana tuhumar laifi, to me ya sa babu wata ƙara da aka kai kotu? Kuma ko da hukumar EFCC na bincike ne, ba laifi ba ne hakan, me ya sa aka dauki hakan a matsayin hukunci kai tsaye? Muna rayuwa a kasa da ake daukar jita-jita a matsayin hukunci, wannan ba adalci ba ne, fitina ce da aka daure mata gindi da alama.

Kasancewar kamfanin AA&R Investment Group yana hulda da NNPC tun kafin zuwan Ojulari ya isa ya rusa dukan ginin da ake kokarin ginawa na zargi. Ko da kuwa mamallakin kamfanin yana da dangantaka da iyalan wani dan siyasa, hakan ba ya nufin an karya doka ba, Idan wannan ne kuskure, to babu wata hulda da za ta tsira a Najeriya.

Abin damuwa ma shi ne, yadda aka mayar da jita-jitar binciken EFCC zuwa hukuncin laifi. Har yanzu babu wata ƙara da aka shigar gaban kotu, balle a samu hukunci.

Amma labaran da suka ginu akan “ana binciken shi” sun bazu fiye da labaran da suka nuna nasarorin da ya samu. Wannan salon “kisa ta kafar jarida” yana mayar da ƙasar nan ta zama wuri da ba za a iya gudanar da sauyi ba.

A gaskiya, tarihin Ojulari ya fi kowace jita-jita magana. Daga jagorancinsa a SNEPCo har zuwa shigar da sabbin tsare-tsare a NNPC, ya nuna cewa cancanta ce ta kawo shi, ba siyasa ba.

Ya yi alkawari ga kasar nan, ba ga wata kungiya ko wata alaka ba.

Wadanda ke kokarin zubar da mutuncinsa ba sa kokarin kare Najeriya, suna kare kansu ne daga sauyin da ya kawo. Ojulari na matukar barazana ga tsarin da ya zamo hanyar amfana ba bisa ka’ida ba.

Kuma saboda haka ne suka koma boyayyun kokari da bata suna, da fatan za su gaji da karfin bin gaskiya.

Ya kamata mu sani cewa, Najeriya ba ta da sarauta da ke gina kan aminci ko soyayya kawai. Najeriya ƙasa ce ta doka, kuma dokar ta ce ya kamata ta yi jagora, ba hayaniya da jita-jita ba.

Bashir Bayo Ojulari bai cancanci wannan harin na sharri ba. Cancanta da gyaran da ya kawo su ne ya kamata su zama abin yabawa, ba abin suka ba.

Lokaci ya yi da za mu kare ’yan Najeriya masu kishin kasa da kwazon aiki, ba mu yarda da rudin masu son komawa tsarin da ba ci gaban kasa ba.

A karshe, Ojulari ba matsala ba ne, mafita ne. Kuma idan muka kyale a rugurguje shi da boyayyun magana da hasashe marasa tushe, za mu tabbatar da abin da tarihi ya dade yana nuna mana: cewa Najeriya ƙasa ce da ke kin canji, amma tana kuka da rashin ci gaba.

Kima na da rauni, aminci ma haka. Amma a rubuta cikin tarihi: inuwa ba ta iya gurbata rana. Ojulari yana tsaye ba saboda shi cikakke ne ba, amma saboda ya zaji yin abin da ya dace.

A irin wannan lokaci, yin daidai abin tsoro ne. Shi ya sa ake jin tsoron sa.

Amma gaskiya za ta bayyana. Tarihi zai bayyana wane ya yi gaskiya da wanda ya nemi hana canji. Rana ta kusa bayyana. Kuma in har muka bar wannan ɗan Najeriya mai kwazo ya fadi, to ba saboda ya gaza ba ne, sai dai saboda ya ki gazawa a gaban marasa kishin kasa.

A bar Ojulari ya yi aikinsa. A bar gaskiya ta ci nasara. A bar rana ta fito.

Mohammed ya rubuto ne daga Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *