Alfijr
Alfijr ta rawaito kungiyar Masu Ƙungiyoyin Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa ta dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Yahaya Surajo har sai baba-ta-gani.
Hakan ta biyo bayan halin da ya nuna a lokacin wasan mako na 31 da ƙungiyar ta buga da Dakkada FC a Kano a jiya Alhamis.
Wani faifan bidiyo ne, ya karade shafukan sada zumunta, inda aka hangi Surajo ya kai wa wani mataimakin alkalin wasa naushi a wasan, lamarin da kungiyar ta bayyana a matsayin abin takaici, wanda ba za ta amince da shi ba kuma hali da zai iya bata mata suna.
Alfijr
“Don haka ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta kasa ta dakatar da shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Yahaya Surajo daga dukkan ayyukan kungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin,”
Ƙungiya ce da ta hada da hazikan masu kula da kwallon kafa wadanda suka yi fice a fagage da dama na fannin rayuwa da ake sa ran za su ba da horo sosai wajen gudanar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban-daban.
Alfijr
Kungiyar ta fusata kan halin Surajo wanda ya zo kasa da sa’o’i 48 bayan wani taron hadin gwiwa da LMC, inda ta yi gargadi game da ayyukan da za su iya haifar da mummunan zato ga gasar.
Shugaban kungiyar Barr. Isaac Danladi, ya ce ciyaman ɗin na Kano Pillars zai fuskanci kwamitin ladabtarwa don kare kansa kafin a sake shigar da shi cikin kungiyar.
Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa