Da Ɗumi Ɗuminsa! Tinubu ya Nada Sabon Shugaban Hukumar EFCC

FB IMG 1693849912844

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya nada Mista Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Alfijir Labarai ta rawaito Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai ga Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Nadin Olukoyede ya biyo bayan murabus din Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa bayan dakatar da shi.

Tinubu ya kuma amince da nadin Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tsawon shekaru biyar, kafin majalisar dattawa ta tabbatar da su.

Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin Hukumar da su tabbatar da sun yi aiki tukuru.

FB IMG 1697111617018

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *