Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon Kasa (EFCC) sun kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowo, bisa zargin karkatar da naira tiriliyan 1.3.
Alfijir labarai ta rawaito an bayyana wannan kuɗaɗen da cewa wani bangare ne na kaso 13 cikin 100 da aka ware wa jihohin da ke samar da mai.
Bisa ga bayanan wasu na kusa da binciken, ana zargin an karkatar da kudaden ne tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023. An kama Okowa ne a ranar Litinin a birnin Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, lokacin da ya amsa gayyatar EFCC bisa wannan zargi.
Wata majiya ta bayyana cewa an fara bincikar tsohon gwamnan kan wasu kudaden naira biliyan 40 da ake zargin an yi amfani da su wajen sayen hannun jari a kamfanin UTM Floating Liquefied Natural Gas — wani wurin sarrafa iskar gas mai ruwa da kamfanin UTM Offshore Limited ke samarwa a jihar Akwa Ibom.
An bayyana cewa tsohon gwamnan ya kasa bayar da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kudaden. Hukumar EFCC tana bincikar Okowa kan zargin karkatar da wasu kudaden “don sayen gidaje a Abuja da Asaba.”
Okowa, wanda yake tsare a wurin ajiye wadanda ake zargi na EFCC a Fatakwal, ya kasance gwamnan jihar Delta daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj