Faransa Ta Hana Mata Sanya Abaya A Makarantun Kasar

Daga AAminu Bala Madobi

Gwamnatin Faransa ta haramtawa dalibai mata a makarantun gwamnatin kasar sanya Abaya a kan rigunan da wasu mata musulmi ke sanyawa.

Alfijir Labarai ta rawaito Gabriel Attal, ministan ilimi na Faransa ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na TF1 na Faransa a karshen mako.

Ya siffanta abaya a matsayin “karimcin addini, da nufin gwada juriya zuwa wurin da bai dace ba wanda dole ne makaranta ta dauki mataki”

“Lokacin da kuka shiga cikin aji, bai kamata ku iya gane addinin ɗaliban ba kawai sai dai ta kallonsu,” in ji Attal.

“Na yanke shawarar cewa ba za a iya saka abaya a makarantu ba.”

Kasar Faransa dai na da tsauraran dokar hana alamomin addini a makarantun gwamnati da kuma gine-ginen gwamnati, bisa hujjar cewa sun saba wa dokokin duniya.

A shekara ta 2010, gwamnatin ta kuma zartar da dokar hana rufe fuska, matakin da ya janyo suka daga al’ummar musulmi.

Ana sa ran sabuwar dokar ta abaya za ta fara aiki ne daga ranar 4 ga watan Satumba da za a fara sabuwar shekara a Faransa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *