Farfesa Adamu Gwarzo Ya Nemi Goyon Baya Da Haɗin Kan UNESCO-REF Domin Aiwatar Da Yarjejeniyar Dake Tsakani

Alfijr

Alfijr ta rawaito Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya nemi goyon baya da hadin kan kungiyar UNESCO (UNESCO-REF) wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattabawa hannu a makon jiya a tsakanin kungiyar da kuma Jami’ar.

Jami ar MAAUN da UNESCO-REF a ranar Alhamis, 16 ga watan Yunin 2022, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kulla alaka domin ci gaban jami’ar.

Alfijr

Farfesa Gwarzo ya yi wannan kiran ne a wani taron kulla alakar da shugaban hukumar ta UNESCO-REF, Prince Abdulsalami Ladigbolu da sauran manyan jami’an jami’ar a Kano a ranar Larabar 22 ga watan Yuni, 2022.

Ya ce kiran ya zama wajibi bisa la’akari da manufar kafa Jami’ar ta wuce Nijeriya da Afirka ma baki daya domin burin wanda ya kafa jami’ar ta MAAUN shi ne; ta zama daya daga cikin mafi kyawun jami’o’i a duniya.

Alfijr

Ya ce burin daukacin mahukuntan Jami’ar shi ne su tabbatar da cewa hadin gwiwar ya zama daya daga cikin mafi kyawu ta yadda za a samar da ingantaccen ilimi domin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasa.

A cewarsa, ingantaccen ilimi shi ne mafi kyawun abin da za a iya barwa matasan kasar.

Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran munanan ayyuka da suka addabi al’umma na faruwa ne sakamakon rashin ingantaccen ilimi da wadataccen ilimi a tsakanin matasa.

Alfijr

Tun da farko a jawabinsa na maraba, shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya bayyana cewa, yarjejeniyar za ta taimaka sosai wajen inganta huldar kasa da kasa da kuma hangen nesa da manufar UNESCO-REF.

A nasa jawabin, shugaban UNESCO-REF, Prince Abdulsalami Ladigbolu, ya ce UNESCO-REF ta himmatu wajen inganta abubuwan da ake da bukata a tsakanin matasan Nijeriya ta hanyar shirye-shirye da ayyuka daban-daban na duniya wadanda suka dace da abin da ya fi muhimmanci da kuma burin kasa.

Alfijr

Ladigbolu ya zo MAAUN Nijeriya dake Kano ne domin tabbatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattabawa hannu a tsakanin jami’ar da UNESCO-REF.

Ladigbolu, wanda ya yi dogon jawabi a kan bangarori daban-daban na shirye-shiryen UNESCO-REF, ya ce kungiyar ce daya tilo da ke inganta ayyukan ma’aikata na kanta, yana mai jaddada cewa hakan na kara inganta hulda da kasashen duniya.

Alfijr

A cewarsa, manufar ita ce rage bautarwar zamani a tsakanin daliban da suka kammala karatunsu inda suke da damar cin gajiyar muhimman fannoni hudu na yarjejeniyar fahimtar juna.

Ya lissafta bangarorin kamar; bangaren zurfin tunani, jagoranci da inganta karfin tattalin arziki kari kan tattalin arzikin zamani.

Shima a nasa jawabin Mukaddashin Daraktan tsare-tsare na ilimi da tabbatar da inganci, Dakta Nura A. Yaro ya ce da alama UNESCO-REF da MAAUN suna kokarin cimma manufa daya ne.

Alfijr

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin abokan huldar biyu za ta samar da sakamako mai amfani ga dalibai da ma’aikatan jami’ar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaba bangaren Gudanarwa/ Magatakarda, Dr. Habib Uwais, mashawarcin fasaha ga wanda ya assasa Jami’ar, Dr. Hamza Garba, Dr. Abdullahi Garba na Makarantar Kimiyyar zamantakewa da Gudanarwa da Engr. Bashir Garba, shugaban riko, bangaren hulda da kasashen duniya da hadin gwiwar jami’ar da dai sauransu.

Slide Up
x