Kamfanin Man Fetur na Ɗangote ya sanar da cewa gidajen mai da ke sayen fetur daga matatar sa za su fara sayar da litar fetur kan N739 a jihar Lagos, daga ranar Talata.
Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Ɗangote, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lagos.
Ɗangote ya tunatar da jama’a cewa a baya-bayan nan kamfanin ya rage farashin fetur daga N828 zuwa N699, a wani ɓangare na ƙoƙarin rage raɗaɗin hauhawar farashi ga al’umma.
A cewarsa, sabon tsarin farashin na daga cikin matakan da matatar Dangote ke ɗauka domin daidaita samar da man fetur a cikin gida.
Ya kara da cewa sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 11 ga Disamba, kuma wannan shi ne karo na 20 da matatar Dangote ke rage farashin fetur a cikin shekarar nan.
Ɗangote ya ƙara da cewa kamfanin ya kuduri aniyar tabbatar da cewa farashin litar fetur ba zai wuce N740 ba a faɗin ƙasar nan a cikin watan Disamba da Janairun 2026.
Attajirin ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙa wa ’yan Najeriya wahalhalun rayuwa, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t