
Alfijr ta rawaito wata Gobara ta kone gidan Gwamnan Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kurmus.
SOLACEBASE ta tattaro cewa kaddarorin gwamnan mai barin gado ya koma cikin makon da ya gabata a kan hanyar Miagun, bayan Kano Club, Nasarawa GRA, a yammacin ranar Litinin.

Majiya mai tushe ta shaida wa SOLACEBASE cewa gobarar da ta tashi daga sashin da Dakta Ganduje ke kiwon shanu da sauran dabbobi gaba daya ta lalata komai, kuma da yawa daga cikin dabbobin sun mutu a gobarar, tare da kona wasu kadarori na miliyoyin naira.
“Ba a dai san musabbabin tashin gobarar ba, amma ta tashi ne a lokacin da ake yin walda da karfen da aka yi a gidan, a dai dai lokacin da ake ci gaba da aikin mayar da wurin ya zama mazaunin da ya dace da gwamnan jihar Kano mai barin gado,”

Ɗaya daga cikin majiyoyin. yace, “Kun ga gyaran ya zama dole domin Gwamna Ganduje bai ji dadin yadda majalisar ta yi ba wanda ya kai ga korar ma’aikatan gidan kusan mutanen 21.”
Da aka tuntubi babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya shaida wa manema labarai, a ranar Alhamis cewa ba ya cikin gari don haka bai san abin da ya faru ba.
Anwar ya yi alkawarin yin magana da gwamnan game da lamarin, sannan ya sanar da lamarin.
Da yake zantawa da wakilin SOLACEBASE, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, wanda ya tabbatar da barkewar gobarar, ya ce tuni aka shawo kan gobarar a lokacin da ‘yan kwana-kwana suka isa gidan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Allah y kyauta
Allah ya qara inama tacinye duka gidan Yanda ya kwacemana filayanmu danmu marayune hakama imaninsa zaikone Azzalimi