Gwamna Kano ya raka tagwayen da ke manne da juna wadanda Saudiyya ta dauki nauyin raba su

Gwamnan Kano

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudiyya kan daukar nauyin yin tiyatar raba tagwayen da aka haifa manne da juna a jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Abba ya yi wa tagwayen da iyayensu rakiya zuwa filin jiragen sama na Malam Aminu da ke Kano, inda suka tashi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya da za a yi musu aiki a can a ranar Litinin.

A yayin rakiyar tasu, gwaman ya gode wa Sarki Salman na Saudiyya a kan wannan kokari, tare da addu’ar Allah Ya biya shi.

Gwamnan ya kuma tuno da yadda ba a dade ba da wasu likitocin kasar Saudiyyan suka je Asibitin Koyarwa na Aminu Kano suka yi wa masu fama da ciwon zuciya da na idanu aiki a kyauta.

Ya yi wa jariran fatan a yi musu tiyata cikin nasara su koma koma gida lafiya a matsayin lafiyayyu.

Da yake nasa jawabin, babban jami’in karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Kano Shiekh Khalil Al’adamawi, ya bayyana cewa irin wannan shiri yana nuna kokarin da Saudiyya ke yi wajen kyautata jinkan al’umma da kuma sadaukarwa ga mabukata.

Abba Gida Gida da jakadan Saudi
Abba Gida Gida da jakadan Saudi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *