
Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sha kuka raɓe-raɓe a ya yin da ya jagoranci zaman majalissar na banƙwana da ƙwamishinoninsa da masu bashi shawara da sauran ma’aikata a fadar gidan gwamnatin jihar Katsina.
Da yake jawabi Gwamna Masari ya bayyana cewa wannan ba kukan barin duniya bane kuka ne na jimamin rabuwa da abokan aiki a tsawon shekaru taƙwas da suka yi a tare don ciyar da jihar Katsina gaba.

“A rahoton da muka samu ya bayyana cewa Gwamna Masari, ya fice daga zauren majalisar, sakamakon yadda hawaye cika masa ido suna rinjayarsa domin ya kasa dannewa daga barin kukan.
A ƙarshe Gwamna Masari, ya godewa ƴan majalissar zartarwar akan goyon baya da gudunmawar da suka bashi waje cimma manufofin gwamnatinsa.
Katsina Reporters
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Allah Sarki dama haka sabo yake.
Hum dadina da duniya kenan, mutum yagama duk ikon daya iya tananan tana mashi kallon wawa