Gwamnan Kano Ya Naɗa Muƙaddashin Sakataren Yaɗa Labaransa


Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Malam Hisham Habib a matsayin muƙaddashin babban Sakataren yaɗa labaransa kafin jiran dawowar mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda zai bar Najeriya ya jagoranci tawagar yaɗa labaran Kano zuwa aikin Hajjin bana.

Hisham, ƙwararre ne kan harkokin yaɗa labarai wanda ya shafe sama da shekaru ashirin yana aikin yaɗa labarai.

A kwanakin baya Hisham ya riƙe muƙamin daraktan yaɗa labaran kwamitin yaƙin zaben jam’iyyar NNPP a zaɓen bana a jihar Kano.

Wannan sanarwa na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai.

Ana sa ran Hisham Habib zai karɓi sabon mukamin na rikon kwarya nan take, gwamnan ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai da su ba shi cikakken goyon baya da hadin kai kamar yadda ya bai wa Bature Dawakin Tofa.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *