Gwamnatin jihar Kano ta fara rabon tallafin kayan abinci da kayan aikin gona ga talakawa mata da manoma a ƙananan hukumomin jihar 44 a yau Litinin.
Alfijir Labarai ta rawaito gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin a ne a shalkwatar hukumar aikin gona da cigaban karkara ta jihar Kano (KNARDA) da ke ƙaramar hukumar Nassarawa.
kayayyakin da za a raba sun haɗa da buhunan shinkafa masu nauyin kilo giram 10 guda 297,000, sai buhunan masara masu nauyin kilo giram 10 guda 160,000, da takin zamani buhu 2,500 sai injin feshi da sauran kayayyakin aikin gona, sannan akwai awaki, da tumaki, da kuma raguna guda 2,600 da za a rabawa mata.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM