Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Makarantu Uku (Principals)

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da wasu shugabannin makarantun Sakandare uku nan take saboda sun kasa aiki.

Alfijir Labarai ta rawaito Makarantun da abin ya shafa sun hada da G.G.S.S. Dawanau, G.G.S.S. Kwa and G.A.S.S. Dawanau duk a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Kwamishinan ilimi na jihar Alh. Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya ziyarci makarantun da misalin karfe 9-10 na safiyar Juma’a, inda ya gano cewa shugabannin da abin ya shafa ba su kai rahoton aikinsu ba.

Daga binciken da ya gudanar, dukkan jami’an ukun sun saba kaurace wa aiki a ranar Juma’a, na wani dan lokaci.

“Wannan gwamnatin ba za ta amince da bata lokaci ba, latti ko kowane nau’i na rashin da’a a hukumance, saboda haka, an dakatar da wadannan shugabannin nan da nan,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a tura sabbi kuma kwararrun shugabanni a makarantun uku nan take, domin tabbatar da cewa ba a dakile ayyukan ilimi ba.

Doguwa ya kuma bayar da umarnin a nemi malamai hudu a GGSS Kwa da biyu a GASS Dawanau a kan ba sa aiki.

“Ayyukan da waɗannan shugabanni da malamai suka yi na nuna rashin muhimmanci.

Mu gwamnati ce da gaske kuma ba za mu bari marasa kishin kasa su lalata mana shirinmu na ilimi ba,” a ya yin gargadin.

A halin yanzu, Kwamishinan ya ba da umarnin cewa shugaban makarantar G.G.S.S. Harbau, karamar hukumar Tsanyawa, a saka mata saboda jajircewarta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Makarantu Uku (Principals)”

  1. Duk yadda akai wadannan mutanen suna da alakar siyasa da Ganduje tunda a karamar hukumar sace, yakamata in da gaskene asamu wasu da aka kora a kananan hukumomin Gwale, Gwarzo, Doguwa kokuma Madobi indai aikin da gaske be.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *