Gwamnatin Kano Ta Kano Ta Dakatar Da Karin Kuɗin Makarantu Da Hana Sayar Da Litattafai Da Uniform

Manufar wannan sabuwar rijistar ita ce tabbatar da sahihin bayanan tsare-tsare na manufofin gwamnati da kuma sanya ido don tsaftace fannin

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da karin kudin makaranta a duk makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu cikin gaggawa.

Haka kuma gwamnati ta dakatar da sayar da litattafai da rigunan makarantu masu zaman kansu.

Kwamared Baba Abubakar Umar, mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin makarantu masu zaman kansu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da yayi da Solacebase a ranar Lahadi.

Baba Umar ya bayyana cewa jihar ta fara bayar da fom na yin rijistar makarantu masu zaman kansu a jihar tun bayan da gwamnati ta sanar da janye shedar aikin makarantar a ranar Asabar.

Ya kuma bayyana lokacin da rajistar zai ƙare ranar Juma’a, 18 ga Agusta, 2023.”

“Manufar wannan sabuwar rijistar ita ce tabbatar da sahihin bayanan tsare-tsare na manufofin gwamnati da kuma sanya ido don tsaftace fannin,” in ji shi.

“Duk abin da muke aiwatarwa na ayyukan makarantu masu zaman kansu a cikin jihar yana daidai da dokar da aka kafa a watan Mayu 2014.”

“Ya kamata iyaye su kai rahoton duk wata makaranta da suka tambaye su karin kudi, saboda an dakatar da hakan a yanzu,” in ji Baba Umar.

“Ba za a bar makaranta ta sake kara kudaden makaranta ba tare da bata lokaci ba.”

Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar za ta kuma tabbatar da cewa iyaye suna biyan ‘ya’yansu kudin makaranta a lokaci guda, domin masu gudanar da ayyukan ba kungiyoyin agaji ba ne.

Mashawarcin na musamman ya kara da cewa masu gudanar da makarantu masu zaman kansu da suka kasa shiga kafin cikar wa’adin za su fuskanci takunkumi idan suka ci gaba da aiki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *