Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Dauran Auren Ƴan Gata A kano

FB IMG 1687883795522

Gwamnatin Kano ta sanar cewa a ranar Juma’ar makon nan, 13 ga Oktoba za a daura auren zawara a karkashin shirinta na auren gata.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Abba Kabir ne ya sanar da ranar daurin auren bayan kammala tsare-tsaren da Hukumar Hisbaha ta jihar ta yi domin daurin auren a ofishinta.

Mutum 1,800 ne za su ci gabajiyar auren gatan, wand suka hada da zawarawa da nakasassu da masu karamin karfi, daga kananan hukumomi 44 ta jihar, kamar yadda gwamnatin ta sanar.

Gwamnan ya yaba da yadda Hisbah ta yi tsarin, musamman ganin yadda auren gatan ya kunshi masu karamin karfi da kuma nakasassu.

Ya kuma yi alkawarin ba wa hukumar duk kulawar da ta dace, inda ya nuna bacin ransa da rashin kammala gine-ginen da ke ofishin hukumar a tsawon shekaru takwas na gwamnatin da ta gabata.

Da yake jawabi, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce lokacin da aka dauki nauyin auren gatan da za a yi ya yi daidai, saboda ya kawo wa masu son aure sauki, sannan zai rage matsalar zinace-zinace.

A Wani labarin kuma Karon farko da Arsenal ta yi nasarar doke Man City a gasar Firimiya cikin shekara takwas.

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *