Gwamnatin Plateau Ta Ƙwace Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu A Jihar

Alfijr ta rawaito Gwamnatin jihar Plateau ta kwace lasisin makarantun masu zaman kansu a fadin jihar bayan wani zama da mahunta suka yi don kawo cigaban ilmi a jahar.

Elizabeth Wampum ita ce
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, ta bayyana hakan a yau Alhamis, tace
an dauki matakin ne bayan gano cewa sama da makarantu 5000 na aikinsu ba tare da shaidar lasisi ba.

Kwamishiniyar ta ce kashi 85 na makarantu 495 masu zaman kansu da aka bai wa lasisi tun da farko basu bi ka’ida ba, kashi 90 na makarantantun basa bin ka’idoji da tsare-tsaren gwamnati,

Alfijr

Ta kara da cewa ta ce ana kuma sanar da al’umma cewa dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar za su sake sabunta lasisin su, za a yi hakan ne domin gano makarantun da ke koyarwa ba bisa ka’ida ba, domin samar da ilimi mai inganci ga kowa.

Makarantu masu zaman kansu makarantune da al umma ke kafawa domin radin kansu, I don neman kudi wasu kuma don kishin ilimin.

Slide Up
x