Hukukar NSCDC Ta Cafke Likitan Bogi Bisa Zargin Mutuwar Mai Juna Biyu

FB IMG 1714720064458

Hukumar tsaron Civil Defence NSCDC, ta samu nasarrar cafke wani likitan bogi, Oladiti Saheed, sakamakon mutuwar wata mai juna a asibitinsa dake jahar Osun.

Alfijir Labarai ta ruwaito hukumar na zargin matashin mai shekaru 32, da bayyana kansa a matsayin kwararren likita, ba tare da ya samu shaidar kwarewa ba wato lasisi.

Dr. Akintayo Adaralewa babban kwamandan jihar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a ranar Alhamis.

Adaralewa, ya ce likitan bogin shaidar karatun Secondary, ce kawai da shi, amma ya karbi mai juna biyun a lokacin da ta fara nakudar Haihuwa, inda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.

Ya kara da cewa, matar ta na dauke da juna biyun watanni tara da makonni uku, wadda ta ziyarci asibitin dake Lamba 2 a unguwar Ororuwa a karamar hukumar Boripe.

A cewar wanda ake zargin matar ta ziyarci asibitinsa ne, sakamakon samun sabani da ta yi da mai gidanta domin ba zata iya ci gaba da zuwa asibitin da aka saba karbar haihuwarta a baya ba.

Ana kuma zarginsa da bayar da horo, ga ma su son zama likitocin bogi kan farashin naira dubu biyar.

Matar ta samu matsala, har aka yi gaggawar kaita asibiti mafi kusa, cikin mummunan yanayi inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

Tuni kungiyar likitoci ta kasa, reshen jahar ta bayyana cewa, ba jami’in lafiya ba ne kuma bai yi rijista da su ba.

A karshe hukumar ta ce da zarar an kammala gudanar da bincke zata gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *