Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Samu Nasarar Kubutar Da Rayukan Mutane 8 Da Tarin Dukiya A Jihar

Hukumar kashe gobar ta jihar Kano Kar kashin jagorancin Babban Darakta Alh. Hassan Ahmad Muhd ta gudanar da aiyuka a daukacin ofisoshi 28 da hukumar ke dasu a fadin jihar cikin watan Juli da ya gabata,

Alfijir Labarai ta rawaito gagaruman ayyukan da ta gabatar sun hada da :-

  1. Kiran gobara guda 25
  2. Kiran neman agajin gaggawa guda 11.
  3. Kiran karya guda 4.
  4. Dukiya da aka rasa sanadiyar ibtila’in gobar # 14,350,000.
  5. Dukiyar da muka samu nasarar ceratarwa daga ibtila’i daban daban 31,000,000.
  6. Acikin watan Bakwai daya gabata an rasa rayukan mutane 3 sanadiyar ibtila’i daban daban.
  7. Mun samu nasarar tseratar da rayukan mutane 8 daga ibtila’i daban daban.

Daraktan ya kara da cewa, zan yi amfani da wannan damar don Jan hankalin alumma dasu kula a yayin amfani da wuta don kaucewa ibtila’in gobara, da Kuma Jan hakali ga masu amfani da tukunyar iskar gas na girki a jikin ababan Hawa da na’urar janareto.

Hakazalika muna shawartar masu amfani da ababan Hawa dasu nemi Tukunya da iskar (CNG) Don kaucewa faruwar iftila’in gobara.

Jan hankali ga masu tuka ababan hawa da suyi tuki cikin nutsuwa don kaucewa faruwar hadarin kan hanya.

Bayan haka muna Jan hankalin al-umma da su gyara magudanan ruwa, duba da yanayin damuna da Mike ciki dan kaucewa faruwar ibtila’in ambaliyar ruwa.

Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar PFS. Saminu Yusif Abdullahi ya sanyawa hannu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *