IGP ya kira taron gaggawa don magance kura-kuran da suka tafka wajen kama yara yayin zanga-zanga

IMG 20241007 WA0012

IGP ya kira taron gaggawa don yin nazari da gyara kura-kurai wajen tsare masu laifi bayan ganin yadda yan Najeriya suka yi ca kan abunda aka yiwa yara yan zanga-zanga a lokacinda suke tsare a hannun yan sanda

Alfijir labarai ta rawaito shugaban yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya karbi rahoton bincike na musamman da yasa aka yi masa dangane da halin da yara yan zanga-zanga suke ciki musamman zargin rashin kulawa da su a lokacin da suke tsare a hannun yan sanda,

“Bayan samun rahoton binciken IGP ya sha alwashin yin nazari sosai tare da daukar matakan da suka dace don magance aukuwar irin haka a gaba na duk wata ɓaraka ko sakaci da aka samu”

Shugaban yan sandan ya kuma yi kira a wani babban taro na DCs da CID da shugabannin Rukunonin Bincike na yan sanda zuwa wani taron bita a ranar 7 ga watan Nuwamba a Abuja, domin kara wa juna sani da baiwa yan sandan horo na yadda za su sake samun ƙwarewa wajen bincike musamman abun da ya shafi masu ƙarancin shekaru” inji sanarwar

A Yau

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *