Jami’an Yan Sandan Kano sun Cafke Yan Daba Da Muggan Makamai 29 Yayin Bikin Mauludi

FB IMG 1696660118260

Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke wasu yan Daba 29 a lokacin bukukuwan Takutaha a jahar, inda aka samu wukake 19, Almakashi guda 2, Danbida 2 da kuma kwaya.

Alfijir Labarai ta rawaito Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya godewa al’ummar jahar Kano bisa hadin kan da suke bawa rundunar  akoda yaushe.

Wannan na zuwa bayan umarnin da sufeton yan sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu Egbetakun , ya bada umarnin ga dukkanin dakarun yan sanda da suke aike a fadin Nijeriya, kan cewa a tabbatar da an bada tsaro lokacin gudanar da bukukuwan Maulidi baki daya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar yan sandan jihar Kano ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yammacin ranar juma’a.

Kiyawa ya ce rundunar yan sandan jahar Kano, bata tsaya a baya ba, wajen bayar da tsaro dan ganin an gudanar da bikin Maulidin lafiya baki daya.

Ya kara da cewa daga ranar 3 ga watan Oktoba 2023, rundunar ta samu nasarar kama matasa 29 , wadanda mafi yawancin su yan daba ne da kuma masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.

FB IMG 1696660364980
FB IMG 1696660353172
FB IMG 1696660373843
FB IMG 1696660348999
FB IMG 1696660345707

A karshe rundunar ta bayyana cewa da zarar ta kammala bincike za su gurfanar da su, a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *