Jami’ar Bayero Kano Ta Kori Dalibai Guda 27


Alfijr ta rawaito Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta kori dalibanta 27, ta kuma dakatar da wasu takwas da ta samu da aikata magudin jarabawa.

Jami’ar ta bayyana hakan ne ranar Lahadi cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktar Sashin Jarabawa da Dauka da Adana Bayanan Dalibai (DEAR), Amina Umar Abdullahi.

Daraktar ta ce hakan ya biyo bayan zaman da majalisar malaman jami’ar ta gudanar ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2023.

Haka kuma a cewarta matakin ya yi daidai da sashi na 20.17 (Ai, iii, iv, v, vi, vii, x da na xii) na dokar jami’ar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *