Jawabin mai ɗakin shugaban kasa yayin miƙa ɗaliban da aka sace a jamiar Dutsin-Ma ga iyayensu

IMG 20231218 102403

Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta mika ɗalibai mata na Jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da aka sace kwanakin baya hannun iyayensu.

Alfijir labarai ta rawaito an kuɓutar da ɗaliban ne sakamakon aikin haɗin guiwa tsakanin jami’an tsaro ƙarƙashin kulawar ofishin mai bawa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro (NSA).

Yayin da take karbar ɗaliban su biyar na jami’ar ta Dutsinma da aka ceto, wadanda ƴan bindiga su ka yi garkuwa dasu, Sanata Oluremi ta ce ilimi shi ne babbar hanyar yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya.

Sanata Remi Tinubu ta bayyana godiya ga jami’an tsaro da suka yi aikin ceto ƴan matan tare da kira ga ɗaliban da kada su bari abinda ya faru ya kashe musu guiwar neman ilimi.

Mai ɗakin shugaban ƙasar ta kuma bada sanar war tallafin karatu (scholarship) na Naira miliyan 1 ga kowace yarinya a cikinsu da sabuwar kwamfutar tafi-da-gidanka a ƙarƙashin tsarin nan na Renewed Hope Initiative (RHI) da take jagoranta.

Hakazalika, ta sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da kuɗi naira miliyan biyu a matsayin tallafi ga iyayen kowacce daga cikin ‘yan matan da aka ceto.

Waɗannda suka halarci taron miƙa ɗaliban sun haɗa da iyayen ‘yan matan da aka ceto, Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya Dutsin Ma, Katsina, Wakilin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da wakilin NSA.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *