Kadan daga cikin alheran da ya kamata ku sani game da marigayi janar Abacha – Alfijir Labarai

📸Abacha Family

Janar Sani Abacha, an haife shi ne a ranar 20 ga Satumba, 1943, shi ne shugaban mulkin soja na Najeriya daga ranar 17 ga Nuwamba, 1993 zuwa 8 ga Yuni, 1998 a lokacin da Allah ya karɓe shi kwatsam.

janar Abacha
janar Abacha
  1. Janar Abacha dan kabilar Kanuri ne, dan asalin jihar Borno, a nan aka haifi shi, kuma ya girma a jihar Kano.
  2. Marigayin ya auri Shuwa Arab, wato Hajiya Maryam, ita ma daga jihar Borno, a shekarar 1965, sun haifi maza shida mata uku. Yaron farko mai suna Ibrahim ya rasu a wani hatsarin jirgin sama a shekarar 1996.
  3. Sun haifi ɗan su na karshe a Aso Rock a shekarar 1994 lokacin Abacha yana da shekaru 50, matarsa, kuma tana da shekaru 47.
  4. Abacha shi ne shugaban kasa na farko kuma daya tilo da bai taba tsallake wani matsayi ba a gidan soja har ya zuwa matsayin Janar na soja.
  5. Biyu daga cikin muhimman shawarwari na taron tsarin mulki na 1995 da ya kafa su ne: kashi 13 cikin 100 na samar da man fetur ga yankunan da ake hako mai da shiyyoyin siyasa guda shida.
  6. Marigayin bai taba rike mukamin soja ba a rayuwarsa har sai da ya zama ministan tsaro a shekarar 1990, daga baya aka sake nada shi sakataren tsaro a 1993, kuma ya kasance Laftanar Janar a lokacin.
  7. Magoya bayansa sun bayyana shi a matsayin mai kula da tattalin arziki kuma ya daidaita farashin canji a kan N22/$1 amma farashin kasuwar bayan fage ya kai N80/$1.
  8. A zamanin Abacha ne Najeriya ta zama mai fitar da man fetur na dindindin, saboda duk matatun man suna aiki. Sai dai kuma bayan rasuwarsa, har yanzu Najeriya ta dogara ne kan shigo da mai daga kasashen waje.
  9. Marigayin shine ya taka rawar gani wajen maido da zaman lafiya da dimokuradiyya a Saliyo da Laberiya bayan shekaru ana yakin basasa.
  10. Janar Abacha ya kafa asusun hada-hadar man fetur (Special) Trust Fund, wanda jama’a suka amince da cewa ya taka rawar gani wajen bunkasa ababen more rayuwa da shirye-shiryen shiga tsakani a fannin ilimi, lafiya da. ruwa.
  11. Marigayin ya karfafi matarsa ta kafa wani asibitin da ake kira National Hospital, Abuja. Tun da farko an sanya masa suna National Hospital for Women and Children kafin daga bisani a daga darajarsa zuwa babban asibitin kasa na daya.
  12. Marigayin yaki amincewa da sharri da makircin turawan yamma ne, ya maida hankalinsa kan ci gaban Afirka da korarin gina kasarsa! Wannan ya saka kiyayyarsa da turawan, domin ya hanasu gaban hantsi.
  13. Abacha shi daya tilo da ya biyawa Najeriya duk tarin bashin da ake bin kasar, na karya dana gaskiya! Amma dake ba wannan ne burin su ba, suka ki karbar Kuɗin, shi kuma yace musu su ajiye kudin idan lokacin da suka biya kansu, su dawo da canji.
  14. Marigayi Sani Abacha shine shugaba daya tilo wanda ya gagari turawan yamma a mulkinsa, duk da kokarin da aka dinga yi na amfani da macuya amana daga makusantansa domin cimmasa!

To babban abinda ya kamata al ummar Najeriya dama duniya su sani shine! Wannan kin amincewar da ya ki yayi da su, kuma ga bashin da suke kokarin a kansa su mai damu bayi, shi yasa suka yi duk mai yiwuwa wajen ganin bayansa, kuma dama wa adinsa ya kare Allah ya karbi rayuwarsa.

Sannan wannan karyar da ake yiwa jahilan cikinmu da kananan yara da kuma marasa kishin arewa hadi da makiyan Najeriya, a irin kudin da marigayin ya biyawa kasar nan bashi suka ki karba ya ajiye musu da zumnar idan lokacin da aka saka za a biya yayi, sai su biya kansu, to fa sune ake debo wasu a kawo da sunan wai ya saci kudi ya kai ya ɓoye, sai kaji karnukan farauta na ta haushi wai kudin daya ya sata! Uhm! kifi na ganin ka mai jar koma.

Abin tambaya anan shine! Ta ina Abacha ya je Turai har a ajiye kudaden da ake cewar ya sata?

Bayan mun tabbatar da tunda ya hau Mulki bai taba zuwa kasashen Turai ba.

Shin ina tarin Kudaden da ya tarawa Najeriya da zummar kawowa kasar ci gaba, kuma ya mutu ya barsu?

Shin ina wadanda ya mayar mutane a tarihin rayuwarsa, shin duk sun manta halascinsa ne ko kuma don suna ganin suna cikin daula kamar ba za su mutu ba?

Allah ya jikan Janar Abacha Allah ya gafarta masa, Allah ya shafe kura-kuransa. Allah ya sa mu yi Kyakkyawan karshe ameen.

Janar
Janar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

One Reply to “Kadan daga cikin alheran da ya kamata ku sani game da marigayi janar Abacha – Alfijir Labarai”

  1. Allah yajikan Baban mu Gen. Sani Abacha Allah ya jaddada musu rahama tare da mahaifin mu. Yayi rawar gani kan tafiyar da mulkin Nigeria hakan tasa sukayi yunkurin ganin bayansa. Tafiya tai tafiya yau shekara 26. In da ya tafi suma zasu je,wasun su ma har sun tafi ,Allah shine mai hukunci tsakanin su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *