Ɗan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha, Sadiq Abacha, ya bayyana girmamawa da alfahari ga mahaifinsa, yana mai cewa shugabancinsa yana da muhimmanci duk da sukar da ake masa har yanzu.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Sadiq ya nuna cewa mahaifinsa ya fuskanci hassada da cin amana a boye, amma ya dage cewa tarihi zai yi masa adalci a karshe.
“Mutumin nan Abacha—kai ne ko yaushe suke wa hassada da mugun nufi. Tarihi zai tunaka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun yi ƙoƙarin bata maka suna. A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai fiye da kowane lokaci. Hakika kai ne mutumin da suke fatan su zama koda rabin irinka ne,” in ji shi.
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ