Karar Kwana! Mutum 4 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kano

Screenshot 20220703 225212 com.facebook.katana edit 11601898971666

Hatsarin mota ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum hudu, wasu da dama suka samu raunuka a kusa da kauyen Dinyar Madiga da ke Karamar Hukumar Takai a Jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ce lamarin ya faru ya yi da wani mai babur dauke da mutum uku ke yunkurin wuce wata motar safa.

Ya ce, “Da isa wurin da lamarin ya faru, jami’an kashe gobara sun gano wasu mutum hudu a sume, inda suka yi nasarar ceto wasu shida ciki har da direban bas din.

“Nan take an ba wa wadanda suka jikkata kulawa a kai asibitin NYSC na Takai, amma daga baya likitoci sun tabbatar da mutuwar mutum hudu,” in ji shi.

Kakakin hukumar, ya gargadi masu ababen hawa da su rika tabbatar da ki’yaye ka’idojin tuki domin kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *